Tsaurin Ra'ayi: Wane Dan Boko Haram ne ya yi Karatun sa a kasar Saudiya?
A yau Jumma'a 19 ga watan Oktoba, Legit.ng ta kawo muku labarin kalubantar da wani babban malamin Sunnah a jihar Kano ya yiwa ikirarin wasu daidaikun al'umma kan cewa kasar Saudiya na horar da ilimin tsaurin ra'ayi na addinin Islama.
Wannan Malamin Dakta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo, wanda shima ya yi karun sa a kasar ta Saudiya ya bayyana cewa, da ace abinda kasar Saudiya take koyarwa kenan shekaru-shekaru aru-aru baya to kuwa da yanzu duniya ba ta zaunu lafiya ba.
Dakta Sani ya yi wannan kalubalantar ne domin kore tuhumar da wasu mutane ke yi na cewa sabon tsarin da Saudiya ta kawo na samar da cibiyar tace ingatattun hadisi hanya ce ta kara horar da tsaurin ra'ayi a cikin addinin musulunci, inda malamin ya ce hakan ba gaskiya ba ne domin kuwa kanzon kurege ne kawai.
Malamin ya ce akwai makamantan sa ba bu iyaka a fadin duniyar nan da suka yi karatun su a kasar ta Saudiya, wanda a halin yanzu ba bu wata kasa da ta yaye daliban addini fiye da kasar ta Saudiya, wanda ya ce da zancen ma su yin wannan ikirari gaskiya ne to kuwa da yanzu wani labari na daban ake yi a kasar nan.
KARANTA KUMA: Bajinta da kwazo ta sanya hukumar sojin kasa ta harba wani karamin soji zuwa babban Matsayi
Legit.ng ta ruwaito daga babban malamin inda ya bayar da misalin cewa, 'yan ta'adda na Boko Haram da suka addabi kasar nan nawa daga cikin su suka yi karatu a kasar Saudiya, ya ce babu ko guda, wanda tsarin ra'ayi ne ya jefa da yawa daga cikin su wannan ta'addanci.
Babban malamin yayin ganawa da manema labarai na BBC ya bayyana cewa, wannan cibiya da hukumomin kasar Saudiya za ta kafa domin tantance ingatattun hadisai, ya samo kudiri ne tun shekaru 20 da suka gabata, inda ya ce wannan yunkuri na kasar Saudiya zai taimaka kwarai da aniyya wajen fito da ma'anonin hadisai tare da hana masu tsarin ra'ayin addini jikitar da ma'anonin su.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng