An gano abun da Jonathan yaje yi gidan Babangida a Minna jiya

An gano abun da Jonathan yaje yi gidan Babangida a Minna jiya

Yayin da al'amurran siyasar kasar Najeriya ke dada kara zafafa ne dai tsohon shugaban kasar nan Goodluck Jonathan ya ziyarci tsohon shugaban kasar a mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida a gidan sa dake a Minna jiya Laraba da rana.

To sai dai tsaffin shugabannin sun tattauna ne a bayan fage kuma cikin sirri inda ba su bari yan jarida sun halarci tattaunawar ba da suka shafe kimanin awanni biyu tun daga karfe 10 na safe har zuwa karfe 12 na rana.

An gano abun da Jonathan yaje yi gidan Babangida a Minna jiya
An gano abun da Jonathan yaje yi gidan Babangida a Minna jiya

KU KARANTA: Yan ta'adda sun halaka sojojin Najeriya 3

Legit.ng dai ta samu cewa jim kadan bayan kammala tattaunawar ta su yan jarida sun tambayi Jonathan din ko me suka tattauna amma sai yace amun sirri ne a tsakanin su amma da suka matsa shine sai yace ya zo ne ya duba lafiyar sa tun bayan zuwa jinyar da yayi a kasar waje.

Haka zalika da yan jaridar suka sake tambayar ra'ayin sa game da harkokin siyasar kasar sai shugaban ya kada baki yace shi yayi ritaya daga dukkan al'amurran siyasar kasar sannan kuma ya jinjinawa yan jaridar kan yadda suke kokari ga ayyukan su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng