Dan wasa Messi ya ci kwallo 100 a wasannin nahiyar Turai
Shahararren dan wasan kwallon kafar nan dan asalin kasar Ajentina watau Lionel Messi a jiya ya cimma wata nasara a tarihin kwallon sa inda ya ci kwallon sa ta 100 a wasannin nahiyar Turai a rayuwar sa ta kwallon kafa a kungiyar Barcelona.
Dan wasan dai ya cimma wannan babbar nasarar ce bayan da ya ci wa kungiyar ta Barcelona kwallo a yayin karawar su da kungiyar Olympiakos inda suka lallasa ta da ci 3 - 1 a gasar Zakarun Turai a ranar Laraba a filin wasan su na Nou Camp.
KU KARANTA: Malaman Firamare sun fara yiwa El-rufa'i azumi
Legit.ng dai ta samu cewa kungiyar ta Barcelona ce ta fara cin kwallo a minti na 18 da fara buga wasan bayan da Dimitris Nikolaou ya ci gidan su a bisa kuskure.
Jim kadan kuma bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci kuma ne sai Lionel Messi ya kara ta biyu sannan wani dan wasan na Barcelona Lucas Digne ya kara na uku.
Mai karatu kuma dai zai iya tuna a jiya ma dai wannan shahararren dan kwallon na kungiyar Real Madrid watau Cristiano Ronaldo shima ya zura tashi kwallon a wani wasan da aka tashi canjaras tsakanin kungiyar Real Madrid da Tottenham duk dai a kasar ta zakarun turai.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Who will win the champions league? ON Legit.ng TV
Asali: Legit.ng