Buhari ya ziyarci kabarin wanda ya kafa kasar Turkiyya, ya kuma gana da Erdogan (hotuna)
- A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari na a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya
- Shugaban kasar ya ziyarci kabarin uban kasar Turkiyya
- Ya kuma hadu da shugaban kasar Tukiyya Recep Tayyip Erdogan
A ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya.
A lokacin ziyarar aiki da ya kai shugaban kasar ya ziyarci kabarin wanda ya kafa kasar Turkiyya, Mustafa Kemal Ataturk.
Legit.ng ta tattaro cewa shugaban kasar ya sanya hannu a wani takardan tarihi don girmama Misaki-i Milli Kulesi a cikin haraban kabarin, da kuma gidan tarihin.
Daga bisani Shugaban kasar ya gana da shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a fadar shugaban kasar.
KU KARANTA KUMA: Babu mutumin da ya fi karfin jam’iyyar – PDP ta maida martani ga Obasanjo
Shugaban Buhari ya samu rakiyan jakadan Najeriya a kasar Turkiyya, Iliyasu Paragalda da wasu manyan jami’an gwamnati guda biyu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng