Rundunar sojin ta tura jiragen yaki da ma’aikatan ta garin Jos domin su wanzar da zaman lafiya
- Rundunar sojin sama ta aika da jiragen yakinta da jami’anta zuwa garin Jos
- Hakan ya biyo bayan rikicin da ya barke a jihar
- Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayar da wannan umurni domin ganin an wanzar da zaman lafiya a yankin
Rundunar sojin sama ta aika da jiragen yakinta da jami’anta zuwa garin Jos, babban birnin jihar Plateau domin taimakawa aikin Operation Safe Heaven don ganin an wanzar da zaman lafiya da kuma hana kashe kashe tre da yaduwar rikici a wasu yankuna na jihar.
Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar ne y aba da umurnin bisa ga umurnin shugaban kasa kuma kwamandan hukumomin tsaro, Muhammadu Buhari domin ganin cewa an kawo karshen kashe-kashe da rikicin da ya taso a jihar.
Haka zalika an tura rundunar ne domin hana hare-hare na daukar fansa, wand aka iya karfafa rikicin. Jiragen yakin da aka tura sun hada da Jirgi mai lamba L-39ZA, jirgi mai saukar ungulu EC-135, wanda zai ba rundunar damar aiwatar da ayyukansu a jihar.
KU KARANTA KUMA: El-rufai ya kira ruwa: Malaman firamare sun fara azumi a Kaduna
Jirgin L-39ZA na aiki daga tushen sa a Kano yayinda jirgi mai saukar ungulu EC-135 ke aiki daga Jos.
Ga sauran hotuna a kasa:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng