Farashin Shinkafa, Gero da Masara ya fadi warwarsa a jihar Katsina

Farashin Shinkafa, Gero da Masara ya fadi warwarsa a jihar Katsina

Farashin kayan gona ya karye a jihar Katsina sakamakon damina mai albarka da aka samu, wanda yayi sanadiyyar manoma yin girbi mai kyau a gonakansu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito farashin acca a bana yayi kasa sosai ba kamar bara ba, inda a bara ana siyar da buhun acca akan N16,000 zuwa N18,000, amma sai ga shi a bana ta sauka zuwa N9,000, inji wani dan kasuwan hatsi, Alhaji Adamu Nalado.

KU KARANTA: Daliban sakanadari a jihar Kano sun yi zanga zanga, sun yi ɓarna mai yawa (Hotuna)

Nalado ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa dalilin da yasa farashin ya tashi a bara shine sakamakon yan kasuwa daga Nijar sun shigo dayawa sun sayi kayan abinci, amma a bana kuma Masara suke bukata, kuma sun same shi a arha.

Farashin Shinkafa, Gero da Masara ya fadi warwarsa a jihar Katsina
Hatsi

Hakazalika farashin masara ma ya sauka, inda a bara ake siyan buhu kilo 100 akan N16,500, amma a yanzu ana samunsa akan N8.500, kamar yadda wani manomi Sani Dandume ya bayyana.

Wani mai kamfanin sarrafa shinkafa a Bakoru, Malam Farouk Abdullah ya tabbatar ma majiyar mu karyewar farashin shinkafa, inda yace sakamakon samun ruwa mai albarka, da kuma isashshen taki, an samu shinkafa dayawa.

Farouk yace buhun shinkafa yar Hausa baya wuce N13,000, inda kuma ake siyar da shinkafar da aka cashe akan N24,000, ba kamar a shekarar data gabata ba, inda ake siyar da shi akan N32,000.

Sai kuma farashin gero, wanda shima aka tabbatar da karyewar farashinsa, kamar yadda wani dan kasuwa Aminu Ibrahim ya bayyana; “Kayan gona sun yi kyau a Katsina, musamman Gero, a yanzu farashin buhu kilo 100 baya wuce N11,500, inda a bara muke siyar da shi akan N20,00.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: