An gurfanar da wani kwarto mai yiwa mata asiri a gaban Kotu
- An shigar da karar ne a wani kotu da ke garin Minna na Jihar Neja
- An yi zargin sa da yin amfani da sihiri wurin neman matar wani
- Ya ne mi yaudarar matar ta hanyar fakewa da ba ta maganin da zata mallake mijin ta
Hukumar 'yan sanda ta gurfanar da wani mai suna Ibrahim Bawa a gaban kotun majistare a garin Minna bisa zargin neman matar wani, wanda yin hakan laifi ne.
Mai shigar da karar, Sifeta Ahmad Sa'idu, ya shaidawa kotun yadda mijin matar me suna Alhaji Tanimu Salihu ya kai masu rahoto a ranar 26 ga watan Agusta.
Tanimu ya bayyana yadda Bawa ke yawan gayyatar matar ta sa cikin dare yana fakewa da zai ba ta maganin mallakan miji.
DUBA WANNAN: Direbobin Tanka sun kulle titin Abuja-Lokoja bayan jami'in karban haraji ya kashe direban tanka
Sai dai kuma Bawa ya musanta tuhumar da ake masa a inda alkalin kotun ya bayar da belin sa akan naira 100,000 tare da masu lamunce masa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng