Yadda ta kaya a wasannin gasar zakarun turai a jiya
A jiya ne dai da misalin karfe 7:45 na yammaci aka kece raini a tsakanin kungiyoyi 16 a cikin wasanni 8 da aka fafata a kasashen daban daban a nahiyar turai a ci gabada da buga kasar zageye na 3 a wasannin rukuni.
To sai dai a wasannin na jiya, kungiyar Liverpool ta lallasa Maribo da ci 7-0 a gasar a wasa mai tarihin da aka zura kwallaye mafi yawa da kungiyar a tarihin gasar tun bayan shekara 10.
Legit.ng ta samu da cewa yan wasan kungiyar Fermino da Mohamed Salah kowanne ya ci kwallo bibiyu sai Coutinho da Oxlade-Chamberlain da kuma Alexander-Arnold da kowanne ya ci dai-dai.
KU KARANTA: 2019: Babu wanda ya kai Buhari nagarta
Sauran wasannin da suka fi daukar hankali kuma sune dai na tsakanin kungiyar Real Madrid ta kasar Sifen da kuma kungiyar Tottenham ta kasar Ingila da aka tashi kunnen doki 1 - 1 bayan.
Ga dai yadda sakamakon wasan ya tashi:
AS Monaco 1 : 2 Besiktas
RB Leipzig 3 : 2 FC Porto
Spartak Moscow 5 : 1 Sevilla
Manchester City 2 : 1 SSC Napoli - Italy
Feyenoord Rotterdam 1 : 2 Shakhtar Donetsk
Apoel Nicosia 1 : 1 BV Borussia Dortmund
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Who will win the champions league? ON Legit.ng TV
Asali: Legit.ng