Dandalin Kannywood: Jaruma Hadiza Gabon na daf da zama amarya

Dandalin Kannywood: Jaruma Hadiza Gabon na daf da zama amarya

Labaran da muke samu daga majiyoyin mu masu karfi da nagarta na nuna mana cewa fitacciyar jarumar nan ta wasannin Hausa fim watau Hadiza Aliyu wadda aka fi sani da Hadiza Gabon na daf da zama amarya bayan da maganar auren ta ta fara karfi.

Duk da dai har yanzu jarumar bata bayyana wanda za ta aura din ba amma dai alamu da kuma kishin-kishin din da muke samu na nuni da cewa tuni jarumar ta tsaida wanda take so ta aura din kuma za a saka rana sha biki nan ba da dadewa ba.

Dandalin Kannywood: Jaruma Hadiza Gabon na daf da zama amarya
Dandalin Kannywood: Jaruma Hadiza Gabon na daf da zama amarya

KU KARANTA: Darussan da na koya bayan an dakatar dani daga majalisa - Ndume

Legit.ng dai ta samu cewa jarumar wadda mahaifinta dan asalin kasar Gabon ne yayin da ita kuma mahaifiyar ta 'yar asalin Jihar Adamawa cewa ta taba tsinka wani a dandalin sada zumunta bayan da ya bata shawarar tayi aure a kwanan baya inda ita kuma ta shawarce shi da ya bawa mahaifin sa shawara ya sakin uwar sa sai ta aure shi.

Jama'a dai dama na ganin sana'ar fim bata kamaci matan ba inda a ko da yaushe sukan ba su shawarar suyi aure su bar harkar don kuma sun fi daraja a dakunan mijin su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng