Siyasar Kano Sai Kano: Ya take ne! Tunda Musa Iliyasu Kwankwaso ya sami matsayin kwamishina a Gandujiyya a yau?

Siyasar Kano Sai Kano: Ya take ne! Tunda Musa Iliyasu Kwankwaso ya sami matsayin kwamishina a Gandujiyya a yau?

A Kano dai, siyasa sai kara juyawa take, yayin da ake fuskantar zabukan 2019, kullum kowanne jigo sai kokarin ya zamo shi ne a sama, mai samari mai kuri'u. Kamar dai an hada kai da Gandujiyya da Shekariyya, domin a tumbuke tushen Kwankwasiyya a badi.

A sabbin nade-nade da gwamna Ganduje yayi na kwamishinoni, inda ya sauke wasu 5 ya dora wasu 6, an gano suna daya da a iya cewa wani makami ne da Malam Shekarau na PDP ya arawa Gandujiyyar domin a 'rafke' Sanata Kwankwaso, a 2019.

Siyasar Kano Sai Kano: Ya take ne, tunda Kwankwaso ya sami matsayin kwamishina a Gandujiyya a yau?
Siyasar Kano Sai Kano: Ya take ne, tunda Kwankwaso ya sami matsayin kwamishina a Gandujiyya a yau?

Sanata Kwankwaso dai sun raba gari da mataimakinsa magajinsa Gwamna Ganduje mai-likimo. Ta kai har a bikin babbar sallar nan mabiya darikun biyu a APC sun yi ma juna rotse, inda aka zubda jini samarin jihar ba gaira babu dalili, kuma ma wai duk 'yan jiha daya, addini daya, kabila daya.

Shi dai Musa Iliyasu Kwankwaso kani ne ga Rabi'u Kwankwaso, kuma basu ga maciji da juna, domin ko da shi Musa Iliyasu yana gidan Shekarau ne, an sa rai ma ko da mataimaki Shekarau din zayyi masa, amma suka ajje shi gefe suka dau ustazai, watakil da zasu iya kawo kujerar a 2011.

DUBA WANNAN: Buhari ne zai fa lashe zaben 2019, inji Aso Rock

Kamar dai a yanzu, zata iya kulle wa Sanata Kwankwaso, a hana shi koda tikitin cikin gida a jam'iyyar APC, a PDP kuma, Malam Shekarau ya sami tikiti na sanatan a bagas. Ko dai Kwankwaso ya koma PDP, ko kuwa ya kafa jam'iyya, don kuwa jam'iyya a tsari, a hannun gwamna take. Zai kuwa yi wuya Sanatan ya ci takarar 2019 ta shugaban kasa, muddin Nasir El-Rufai da Atiku na fafatawa, idan kenan shugaba Buhari bai ce yana so ba.

Siyasar Kano Sai Kano: Ya take ne, tunda Kwankwaso ya sami matsayin kwamishina a Gandujiyya a yau?
Siyasar Kano Sai Kano: Ya take ne, tunda Kwankwaso ya sami matsayin kwamishina a Gandujiyya a yau?

A mahangar masu sharhi dai, siyasar Kano zata dauki ko wanne irin salo da alkibla, kuma makiyan jiya ka iya zamowa masoya a yau, kamar kuma yadda masu soyayya ka iya raba gari, lissaffin 2019 da saura.

Sai dai akwai rawar da uba ga kowa Janar Buhari ka iya takawa, ko zayyi takara ko kuma a'a, yana da karfin nune a Kano, kuma duk da cewa an jiyo cewa ya gwale gwamna a ziyarar da yaso yi a Daura, kamar dai su Tinumbu zasu iya murda hannunsa ya nuna Gandujiyyar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: