Allah ya yiwa Mahaifiyar Sheikh Dr. Isah Ali Fantami rasuwa
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raaji'un
Allah ya yiwa Mahaifiyar Sheikh Dr. Isah Ali Fantami rasuwa a safiyar yau lahadi 15 ga watan Oktoba na shekara 2017 a babban asibitin ƙasa dake Abuja.
Za'a gabatar da janaizar ta bayan an kammala Sallar Azahar a masallacin Annur dake birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA : Arewa kurum Shugaba Buhari ya sa gaba Inji wani Dattijon Kasar Yarbawa
Allah ya jiƙkanta ya kyautata makwanci, ya ba al'ummar musulumai hakurin rashinta,
Sheikh Aliyu Isa Fantami shahrarren malamin addinin muslunci ne kuma shine babbar daraektan ma’aikatar NITDA.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng