Ganduje ya sallami kwamishinoni 5 tare da rantsar da 6 a jihar Kano

Ganduje ya sallami kwamishinoni 5 tare da rantsar da 6 a jihar Kano

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sallami kwamishinonin jihar guda 5 tare da rantsar da wasu sababbi guda 6.

Wadannan kwamshinoni da gwamnan ya sallama sun hadar da; kwamshinan shari'a Haruna Muhammad Falali, kwamshinan kasuwanci Ahmed Rabi'u, kwamshinan kasafin kudi Hajiya Zubaida, kwamshinan aikace-aikace Injiniya Shehu Haruna da kuma kwamshinan kudi Farfesa Kabiru Dandago.

Ganduje ya kuma rantsar da sababbi kamar haka; kwamishinan Shari'a Barrister Ibrahim Mukhtar, kwamishinan aikace-aikace, gidaje da sufuri Injinya Aminu Aliyu, kwamshinan kudi Alhaji Aminu Mukhtar Dan Amu, kwamshinan kasuwanci Alhaji Ahmed Rabi'u, kwamshina aikace-aikace na musamman Musa Iliyasu Kwankwaso da kuma Hajiya Aishatu Jafar Yusuf a matsayin kwamshinan kasafin kudi.

Ganduje ya sallami kwamishinoni 5 tare da rantsar da 6 a jihar Kano
Ganduje ya sallami kwamishinoni 5 tare da rantsar da 6 a jihar Kano

Yayin jawabin sa wajen rantsar da sababbin kwamishinonin, Ganduje ya bayyana cewa nadin wannan kwamishinonin ya zo ne duba da irin cancantar su da kuma amincewar mazabun kowanen su.

KARANTA KUMA: Kungiyoyi 10 masu karfin gaske a Najeriya

Gwamna ganduje ya bayyana cewa, gwamnatin jihar Kano ta yi nazarin akan bukatuwar samar da sabon jini a cikin gudanar da shugabancin ta, wanda shine jigo wajen assasa ci gaba da zai kawo sauyi mai inganci ga rayuwar al'umma.

Ya kuma ja kunnen sababbin kwamshinonin a kan su kiyaye kuma suka kauracewa duk wani nau'i na rashawa a cikin gudanar ada aikin su.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: