Abun da Buhari ya ce cikin wasika zuwa ga Shugaban Kasar Chena

Abun da Buhari ya ce cikin wasika zuwa ga Shugaban Kasar Chena

- Femi Adesina, mai magana da yawun Buhari ne ya bayyana abun da takardar ta kunsa

- Buhari ya na farin cika bisa ga kakkyawar alakar da ke tsakanin Chena da Najeriya

- Ya yabawa chena bisa irin cigaba da ta samu karkashin shugabancin jam'iyyar CPC

Mai magana da yawun Shugaban Kasa Muhammad Buhari wato Femi Adesin ya ce Buhari ya bayyana farin cikin sa game da tarayyan amfanuwa da juna da ke tsakanin Najeriya da Chena.

Sakon da Shugaba Buhari ya aike wa shugaban kasar China cikin wasika
Sakon da Shugaba Buhari ya aike wa shugaban kasar China cikin wasika

Adesina ya ce Buhari ya bayyana farin cikin na sa ne cikin wasikar taya murna da ya aikawa Shugaban Kasar Chena yayin da Kasar ke bikin taron jam'iyyar CPC ta kasar karo na 19.

DUBA WANNAN: Tsageran Neja Delta sun yi barazanar hana hako man fetur

Buhari ya yabawa Kasar Chena bisa kasancewarta abokiyar huldar arziki ga kasashe. Ya kuma ce Kasar Chena ta samu cigaba karkashin mulkin CPC a inda ta zamto madubi ga kasashe masu tasowa.

Shugaba Buhari a madadin daukacin 'yan Najeriya, ya na taya Chena murna bisa ga wannan ci gaba, kuma ya na masu fatan alheri.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164