Abuja: Gwamnatin tarayya ta bada jerin sunayen jihohin da za su amfana daga asusun Bankin Duniya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana jerin jihohin 18 da za su amfana daga tallafin Bankin Duniya
- Wadannan jihohin za su kasance tare da sauran jihohi da suka dade suna cin amfani wannan tallafin
- Manufar wannan tallafin shine don samar da hanyoyi sadarwa ga manoman yankin karkara
Gwamnatin tarayya ta ba da jerin jihohin 18 da za su amfana daga tallafin Bankin Duniya na dala miliyan 500 wanda aka taimaka wa Najeriya.
Shugaban shiri na Rural Access and Mobility Project, RAMP, Ularamu Ubandoma, ya ce, jihohin za su kasance tare da sauran jihohi da suka dade suna cin amfani wannan tallafin wajen raba dala miliyan 500.
Wannan aikin yana ƙarƙashin shirin na Rural Access and Mobility Project, RAAMP3.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Ubandoma ya yi wannan bayani ne a cikin sanarwar sabbin jihohi 18 a karkashin shirin RAAMP3 a birnin Abuja a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba.
KU KARANTA: Gwamnatoci na Kudu sun kasance a lokacin da Buhari ya bukaci Bankin Duniya ta fifita Arewa – Inji Shettima
Ya ce, "Manufar wannan tallafi na Bankin Duniya da bankin Faransa da kuma bankin bunkasa Afirka don samar da hanyoyin sadarwa mai kyau ga manoma na yankunan karkara domin kai kayan amfanin gona zuwa kasuwa don kauce wa hasara”.
"A arewa maso gabas, muna da Borno, Bauchi da Taraba. A arewa ta tsakiya, muna da Filato, Binuwai, Kogi da Kwara. A Arewa maso yamma, muna da Kano, Kastina, Sakkwato da Kebbi. A kudu maso gabas, muna da Abiya da Anambra. A kudu maso kudu, muna da Cross River da Akwa Ibo. A kudu maso yamma, muna da Ogun, Oyo da Ondo. Wadannan sune jihohi 18 daga yankunoni 6 da za su amfana”, inji Ubandoma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng