Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi

Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi

Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen makarantu na alfarma kuma masu nagarta da ‘ya’yan Shugaba Buhari Suka Yi. Sai da akwai babbar ‘yar Buhari mai suna Zulaihat da ta rasu a shekarar 2012 wajen haihuwa sakamakon cutar daji ta jini da ta sha fama da ita.

Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi
Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi

Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi
Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi

1) Fatima: An haifi Fatima a ranar 7 ga watan Maris, 1975. Ta yi makarantar firamare dinta a firamarin Sojojin Sama da ke jihar Legas, ta yi karatun sakandaren ta a Kwalejin gwamnati dake Kaduna wato Government College, Kaduna; sannan ta tafi jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria kafin ta tafi kasar Ingila domin yin karatun babban digiri dinta a harkar kasuwanci.

2) Hadiza (Nana): An haifi Nana Hadiza a ranar 23 ga watan Yuni 1981. Ta fara karatunta ne a Makarantar Essence da ke Kaduna sannan ta tafi Kasar Ingila domin Cigaba da karatunta.

Ta yi Karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Buckingham duk a kasar Ingila sannan ta dawo Kaduna domin yin babban digirinta a fannin Malanta a National Teachers Institute, da ke Kaduna. Tayi digiri dinta na biyu a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic.

3) Safinatu (Lami): An haifi Safinatu ranar 13 ga watan Oktoba 1983. Ta yi karatu a makarantar Essence sannan ta wuce kasar Ingila domin yin karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Plymouth, dake kasar Birtaniya da kuma Jami’ar Arden dake kasar Ingila.

4) Halima: An haifi Halima ranar 8 ga watan Oktoba 1990. Tayi Makarantar Essence sannan ta cigaba a makarantar British School ta birnin Lome dake kasar Togo, Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Leicester duk a kasar Ingila. Daga nan ta dawo makarantar koyan aikin lauya a Najeriya.

5) Yusuf: An haifi Yusuf a ranar 23 ga watan Afrilu. Ya yi karatunsa ne a Kaduna International School; British School ta birnin Lome a kasar Togo, Kwalejin Bellerby’s da Jami’ar Surrey, duk a kasar Ingila.

KARANTA KUMA: Saurayi ya burma kaifi a kirjin wani mutum har lahira a Zaria

6) Zahra: An haifi Zara ne ranar 18 ga watan Disemba 1994. Ta yi karatunta a makarantar Kaduna International School; British School ta birnin Lome a kasar Togo, Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Surrey duk da suke kasar Ingila.

7) A'isha (Hanan): An haifi A'isha a ranar 30 ga watan Agusta 1998. Tayi karatunta a makarantar Kaduna International School.

8) Amina (Noor): An haifi Noor ranar 14 ga watan Satumba 2004. Tayi karatu a Kaduna International School.

Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi
Jerin makarantu da 'ya'yan shugaba Buhari suka yi

Binciken ya bayyana nuna cewa mafi yawancin 'ya'yan shugaban kasar sun yi karatun su ne a makarantar Kaduna International, kwalejin Bellerby's dake kasar Ingila da kuma makarantar British School ta birni Lome dake kasar Togo wato jamhuriyyar Benin.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng