Za a iya magance kaso 80 na cutar makanta - Wani Likitan Ido
Najeriya da sauran kasashen Afirka su na fama da nauye-nauyen al'umma da suke fama da matsakaiciyar cutar idanu da kuma masu fama da cutar makanta, wanda a yanzu akwai fiye da kaso 90 na masu fama da matsalar cututtukan idanu na duniya da suka a nahiyyar ta Afirka.
Wani likitan ido kuma shugaban tiyatar idanu a cibiyar idanu ta Me Cure Eye Centre, Dakta Adeboyega Alabi, shine ya bayyana hakan yayin gundanar da wani shiri akan duban idanu da bayar da magani wanda cibiyar ta su ta assasa domin tunawa da ranar idanu ta duniya.
A kan yi bikin zagoyar wannan rana a duk ranar Alhamis ta biyu da ta fada cikin watan Oktoba, domin inganta karfin gani da kuma kiyaye cutar makanta a kowace shekara.
Domin yin murnar zagayowar wannan rana, cibiyar ta Me Cure cikin gudanar da shirin ta aiwatar da duban marasa lafiyar idanu kyauta a ranar Jumma'a tare da daukewa masu bukatar tabarau na idanu kaso 50 da kuma kaso 25 na ma su bukatar maganin digawa a idanu kudin da za su biya.
KARANTA KUMA: Saurayi ya burma kaifi a kirjin wani mutum har lahira a Zaria
Likitan idanun ya bayyana cewa, ba wai kawai za a iya hana kamuwa da kaso 80 na cutar makantar idanu ba, har magance ta za a iya yi. Ya kuma gargadi masu bayar da kudadensu ga wandanda ba kwararru ba wajen duba lafiyar su musamman cutar glaucoma wadda ita ce jigo wajen assasa cutar makanta.
Ya kara da cewa, sakamakon binciken ta cibiyar kare kamuwa da cutar makanta (International Agency for the Prevention of Blindness, IAPB) ta gudanar, akwai kimanin mutane miliyan 30 dake fama da cutar makanta, yayin da miliyan 260 suke fama da sauran cututtuka na idanu da ba su karasa makancewa ba.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng