Babban bankin Duniya zai yi aiki a Jihohi 18 na Najeriya

Babban bankin Duniya zai yi aiki a Jihohi 18 na Najeriya

- Bankin Duniya zai kashe Dala Miliyan 500 a Najeriya

- Za a tallafawa Jihohi 18 na kasar wajen harkar noma

- Jihohin sun hada da na Arewa da wadanda ke Kudu

Jaridar Premium Times ta na da labari cewa Babban bankin Duniya watau World Bank zai yi aiki a Jihohi 18 a Najeriya.

Babban bankin Duniya zai yi aiki a Jihohi 18 na Najeriya
Jami'an Babban bankin Duniya da Shugaba Buhari

Shugaban gudanar da ayyukan tallafi a kauyuka na Bankin da ake kira RAMP watau Ularamu Ubandoma ya bayyana wannan. Ubandoma yace bankin zai taimakawa wasu Jihohin Najeriya wajen sha’anin noma.

KU KARANTA: Majalisa tayi kira ga Shugaban kasa ya kara albashi

Daga cikin ayyukan da za ayi dai akwai makudan kudi da aka ware daga bankin na Duniya da kuma Bankin Kasar Faransa da ma Bankin nan nacigaban Afrika watau AfDB domin yin hanyoyi na kilomita 500 a Jihohin.

Wadannan Jihohi sun hada da Jihar Bauchi, Borno da Taraba. Sannan kuma akwai Jihar Plateau, Benuwe da kuma Kwara da Jihar Kogi. Haka kuma akwai Jihar Kano, Katsina, Sokoto da Jihar Kebbi. A kudancin Kasar kuma akwai Jihar Abia da Anambra. Jihar Kuros Riba da Akwa Ibom. Sai kuma Jihar Ogun, Oyo da Jihar Ondo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng