Kotu ta daure wani dalilin kara auren karamar yarinya
- A wata kasa an daure wani mutumi saboda ya auri mata biyu
- Wannan mutumi ya auri karamar yarinya ne mai shekara 13
- Hakan ya faru ne a can kasar Zimbabwe ta Afrika kwanan nan
Mun samu rahoto cewa an yankewa wani mutumi hukuncin dauri bayan ya auri karamar yarinya a Kasar Zimbabwe.
Wani Kotu a Kasar Zimbabwe ta yankewa wani mutumi mai shekaru 29 hukuncin dauri bayan ya auri yarinya 'yar shekara 13 a Duniya a matsayin matar sa ta biyu Inji Jaridar Zimnews. Wannan dai ya sabawa dokar kasar ta Zimbabwe.
KU KARANTA: An daure mayakan Boko Haram a Najeriya
Ana karar wannan mutumi da kwanciya da yarinyar da ba ta isa a tara da ita ba. Sai dai a cewar wanda ake zargin yace karamar yarinyar ta amince sa shi kafin wani abu ya faru tsakanin su. Kotu dai tace ko sa su na soyayya yarinyar ba ta mallaki cikakken hankali ba.
Alkali mai shari'ar dai ya yankewa wannan Bawan Allah daurin shekaru 2 a gidan maza amma za a iya yi masa afuwa bayan watanni 6 idan har aka yadda da natsuwar sa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng