Hotunan saurayi da ya hakura da neman aiki ya koma sayar da amala
Zaman kashe wando dai aka ce sai maras wayo, in dai ka tashi ka nema zaka samu, wani bawan Allah da ya gane hanyar neman kudi ya koma sayar da amala a shagon mahaifiyarsa, kasuwanci da yace yana kai masa.
Samun damar taya mamansa aiki ya bashi damar iya tuka amala, da tafiyar da shagon ta a kasuwa, kamar yadda ya dace, inji Adio Lawal, saurayi dan shekaru 35 a jihar Ogun, wanda ya kammala digirinsa a jami'a amma ya rasa aiki.
Maimakon ya koma zaman gida, Lawal kawai sai ya koma zuwa aiki a shagon abincin mamansa, inda yake kasuwancinsa, kuma ya taiyar da harkar iyalansa, kai harma da sauran sabgoginsa na rayuwa, ya dai ce, sayar da amala ya kawo masa mutunci da kima.
'Da wannan sana'a mama ta biya mana kudin makaranta, kuma yanzu haka kannai na biyu ma suna kasar waje suna karatu, duk da dukiyar albarkacin amala' ya kara fadi ga Legit.ng
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019 inji fadar Aso Rock
Duk da dai noma ya karanta a jami'a, Malam Lawal ya ce, idan ya sami jari, zai kara bude dakunan amala ne a wurare domin fadada sana'ar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng