Dandalin Kannywood: Alawiyya ta wasan kwaikwayon 'Dadin Kowa' zata zama amarya

Dandalin Kannywood: Alawiyya ta wasan kwaikwayon 'Dadin Kowa' zata zama amarya

Labaran da muke samu yanzu ba da dadewawa ba nan nuni da cewa fitacciyar jarumar nan ta wasan kwaikwayon 'Dadin Kowa' mai suna Khadijah S. Islam wadda aka fi sani da Alawayya ta na can tana karkare shire-shiren shigewa dakin mijin ta na Aure.

Hotunan gabanin aure na jarumar dai suna ta yawo a yanzu haka a kafafen sada zumuntar zamani irin su Facebook da Tuwita inda take ita da zankadeden mijin nata a tsaye.

Dandalin Kannywood: Alawiyya ta wasan kwaikwayon 'Dadin Kowa' zata zama amarya
Dandalin Kannywood: Alawiyya ta wasan kwaikwayon 'Dadin Kowa' zata zama amarya

KU KARANTA: Rayuwar aure da dadi - inji Fati Ladan

Legit.ng dai a iya dan binciken ta na farko-farko ba ta samu cikakken bayani ba game da shire-shiren bukukuwan auren amma zamu kawo maku cikakken labarin a nan gaba kadan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ma dai wasu daga cikin jaruman na wasan kwaikwayon na Dadin Kowa watau Sallau da Furere ma sun angwance inda kuma bikin nasu ya samu halartar dumbin dubun dubatar magoya baya daga kowane sashe na kasar nan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng