Babban Mawakin Najeriya Davido ya shiga hannun 'Yan Sanda

Babban Mawakin Najeriya Davido ya shiga hannun 'Yan Sanda

- Wani abokin Mawakin nan Davido ya rasu cikin 'yan kwanakin nan

- Ana zargin Mawakin ne da hannu a mutuwar wannan abokin na sa

- Sai dai Davido din ya karyata wannan zargi ta bakin Lauyoyin sa

Kamar yadda labari ke zuwa mana lallai fitaccen Mawakin Najeriya da ake kiran sa Davido ya shiga uku bayan ya shiga hannun Hukuma.

Babban Mawakin Najeriya Davido ya shiga hannun 'Yan Sanda
Fitaccen Mawakin Najeriya Davido a dandali

Babban Mawakin David Adeleke ya shiga hannun 'Yan Sanda ne inda ake zargin sa da ta cewa game da mutuwar wani abokin samu Tagbo Umeike. Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Legas a lokacin Edgal Imohimi ya bayyana cewa Mawakin yayi karya game da rasuwar wannan ta'aliki.

KU KARANTA: Mawakin Amurka Nelly yayi wa wata fyade?

Sai dai wannan hamshikin Mawaki ya karyata wannan zargi ta bakin Lauyoyin sa inda yace ba shi da hannu wajen mutuwar abokin kuma bai bada umarni ayi wani abu da yawa ba. Davido yace shi da kan shi ya taka ya je wajen 'Yan Sanda domin amsa tambayoyi don kuwa bai aikata laifi ba.

Yanzu haka dai Mawakin ya dakatar da wasannin sa domin jimami saboda makokin Marigayin abokin na sa Tagbo Umeike. Dangin mamacin dai sun ce akwai fa ta cewa game da wannan rashi da su kayi yayin da wasu ke ganin dama da wa-la-kin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng