Yan matan Chibok sun zama daliban jami’a a yanzu - Osinbajo

Yan matan Chibok sun zama daliban jami’a a yanzu - Osinbajo

- Yemi Osinbajo mataimakin shugaban kasa yayi Magana akan jin dadin yan matan Chibok da aka saki

- Osinbajo ya bayyana cewa a yanzu haka yan matan na karatu a wani jami’a wanda bai bayyana sunan sa ba

- Ya kara da cewa suna jin dadin sabuwar rayuwar su

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa yan matan Chibok da aka saki suna karatu a wani jami’a.

Osinbajo bai ambaci sunan jami’ar ba amma yace: “Muna farin cikin sanar da cewa suna nan lafiya, suna matukar farin ciki da sabon dama da suka samu sannan kuma sun fara sabuwar rayuwa mai cike da aminci.

Yayi magana a fadar shugaban kasa a jiya yayinda ya karbi bakuncin tawagar kungiyar kare hakkin yara mata daga makarantu daban-daban a Abuja, wanda jami’an hukumar ilimi da kuma UNFPA suka jagoranta.

KU KARANTA KUMA: El-Rufai ya bayyana yadda za’a cimma sake fasalin al’amuran kasa

Ya jadadda jajircewan gwamnati na ganin an saki sauran yan matan Chibok da aka sace tare da aika sako ga sauran duniya cewa baza’a yarda da irin wadannan ayyukan ta’addanci na sace mutane a kasar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng