Labari Cikin Hotuna: Yadda 'Yan Najeriya ke yin Zarra a musabakar Alkur'ani ta duniya
Cikin shekaraun da suka gabata, 'yan Najeriya da dama su kan yi fintinkau a wajen gasar karatun alkur'ani ta duniya. Legit.ng ta samu rahoton cewa, wasu 'yan Najeriya sun sake yin zarra da kece raini a gasar karatun Kur'ani ta duniya da aka gudanar a kwana-kwanan a kasar Saudiyya.
Wadannan zakakurai biyu da suka wakilci Najeriya a gasar ta Kur'ani da aka kammala yau Laraba 11 ga watan Oktoba a can kasa mai tsarki a matakai kala biyu, sun yi namijin kokari yayin da kowanensu ya zo ta biyu a cikin matakan.
Akwai Faisal Muhammad Auwal daga jihar Zamfara wanda wakilci Najeriya a matakin gasar zubar da hadda ta izifi sittin tare da tafsirinsa, ya yi fintikau inda ya zo na biyun wani dan kasar Saudiya a wannan mataki.
KARANTA KUMA: Kudaden da aka karbo wajen masu satar dukiyar gwamnati na shiga cikin kasafin kudi na 2017- Gwamnatin Tarayya
Sai kuma Albashir Goni Usman daga jihar Borno, ya wakilci Najeriya a matakin zubar da haddar Kur'ani izifi sittin ba tare da tafsiri ba, in da shima ya kece raini ya yiwa wani dan kasar Bangladesh ta biyu a wannan mataki.
Wannan hazaka ba ta tsaya a wajen zubar da hadda kadai ba, domin kuwa kasar ta Saudiyya ta yiwa wannan gwaraza gagarumar kyauta, wanda shi hausawa kan cewa yaba kyauta tukwici.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng