Dandalin Kannywood: Har yanzu da sauran kuruciya ta - Rukayya Dawayya
Fitacciyar jarumar nan tsohuwar fuska a fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood watau Rukayya Dawayya ta fito tayi fatali da kiraye-kirayen da jama'a ke yi mata na ta yi aure inda tace ita fa har yanzu yarinya ce karama.
Shahararriyar jarumar da ta taka muyimmiyar rawa a fina-finai da dama tare kuma da bada gudummuwar ta musamman ma wajen habakar masana'antar ta ayyana cewa ita duka-duka yanzu shekarar ta 29 a duniya.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta hana Likitoci aiki a asibitocin kudi
Legit.ng a cikin wani dan nazari da tayi game da zancen nata ta binciko cewa indai har hakan ta tabbata to lallai kenan jarumar tana da shekaru 13 kacal a duniya ne ta fito a cikin fim din Dawayya.
Shi dai fim din Dawayya kamar yadda binciken namu ya tabbatar, an shirya shi ne a shekara ta 2001 wanda yanzu kimanin shekaru 16 kenan.
A lissafi kenan idan aka cire shekaru 16 daga cikin 29 ya zama shekaru 13.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng