Aliko Dangote ya bayyana sirrin nasarorin kasuwancin sa

Aliko Dangote ya bayyana sirrin nasarorin kasuwancin sa

- Shahararren mai kudin Nahiyar Afirika wato Aliko Dangote ya bayyana hanyar da za'a bi don samun nasara a kasuwanci

- Ya yi wannan bayani ne a wani taro da aka gudanar a Claridges na Birnin Landan

A ranar Litini ne shahararren dan kasuwannan kuma wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirika ya bayyana sirrin da ke bayan samun nasarar sa a kasuwanci. A cewar sa nasarar ba ta wuce dogaro da kai da kuma samar wa kai kayan bukatu don sana'anta kayaki.

Ya ce ba zasu sake shigo da wani abu ba daga kasashen waje. Ya yi wannan bayani ne a bainar mataimakin Shuganan Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da wasu manyan 'yan kasuwa na duniya a wani taro da aka gudanar a Claridges na Birnin Landan.

Aliko Dangote ya bayyana sirrin nasarorin kasuwancin sa
Aliko Dangote ya bayyana sirrin nasarorin kasuwancin sa

Yayi bayanin yadda Najeriya ke kokarin samarwa kanta kayakin bukatu don amfanin kanta da kuma sayarwa kasashe. Kayaki wanda a baya Najeriya shigo da su ta ke daga waje, irin su siminti da takin zamani.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: A shirye muke mu sadaukar ran mu domin PDP tayi nasara - Gwamna Wike

A game da noma kuwa, Dangote ya ce sun bada himma wurin noma da sarrafa shinkafa kuma za su yi himma wurin samar da madara. Ya ce Najeriya ta kusa samar da abincin da zai ciyar da fadin Afirika ta yamma.

Bayanai da Dangote ya bayar a wannan taro ya nuna kwarewarsa a harkan kasuwanci a inda ya burge masana kasuwanci da dama a taron.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164