Dandalin Kannywood: Babban buri na a yanzu shine aure - Jaruma Fati Garba
Fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa na Kannywood mai suna Fati Garba ta bayyana cewa yanzu ita babban burin ta a rayuwa shine aure sunnar manzo, kamar dai yadda ta shaidawa majiyar mu a cikin wata tattaunawa ta musamman da tayi da ita.
Jarumar ta kuma bayyana cewa ita tunda ta taso a rayuwar ta tana da matukar sha'awar yin wasan fim din Hausa amma bata samu damar cika burin nata ba sai a yan shekarun nan bayan da ta hadu da Adam A. Zango dake a matsayin uban gidan ta a yanzu.
KU KARANTA: Shekara 3 muna soyayya da Nafisa Abdullahi - Adam A. Zango
Legit.ng ta samu cewa jarumar da yanzu haka take gudanar da shirin nan na bautar kasa ta shaidawa majiyar tamu cewar babban abun alfahari ne a gare ta yanzu yadda take jerawa kafada-da-kafada da manyan shahararrarun jaruman Kannywood din wajen sana'ar su.
Da aka tambaye ta game da jaruman da suka fi bata sha'awa sai jarumar ta ce tana da wanda take so a harkar fim din yanzu haka ma amma ba zata ayyana shi ba sai nan gaba amma kuma acikin jarumai mata tafi son Ai'isha Tsamiya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng