Labarai cikin Hotuna: Matashi yayi fasahar kera jirgin sama a jihar Yobe
Legit.ng ta samu rahoton wani mazaunin unguwar Babban masallaci dake karamar hukumar Geidam a jihar Yobe, da Allah ya bashi baiwa ta fasahar kera jirgin sama da har yake iya tashi.
Wannan matashi Hussaini Bukar mai shekaru 23 da haihuwa, ya kera jirgin saman ne da karafa, notina da kuma injina masu baiwa wannan jirgin ikon tashi.
Hussaini ya zayyano cewa, yayi amfani da karafen alminiyo wajen kera jikin jirgin tare daurewa da notina. Ya sanyawa jirgin haske domin haskaka ciki da wajensa da sanya masa injina da har yake iya tashi sama.
KARANTA KUMA: Evans ya ci gaba da yadda yake so a gidan kurkuku
Yayi amfani da filaya tare da sukun direba ta daure noti wajen kirar jirgin, sai dai ya bayyana cewa bai samu damar yin karatun boko ba sakamakon bin umarnin mahaifansa.
Da yawa daga cikin al'umma mazauna unguwar da wannan matashi yake, sun jinjina ma sa kuma sun ce wannan fasahar baiwa ce daga Allah saboda haka babu abin da ya kamace shi face ya yi godiya a gare shi.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng