Duniya ina zaki damu: 'Yan sanda sun gano gawar wani dattijo dan shekara 69 da aka sace a bara
- Kasancewar mutumin tsoho ne mai shekaru 69 bai hana shi shan bugun dawa ba daga hannun wadanda suka sace shi
- Mutumin mai suna Pa Basil Agha ya sha bugu da wasu nau'ukan azaba hannun wadanda suka kama shi
A watan Oktoba na shekarar da ta gabata, da rana tsaka, a ka sace Pa Basil Agha mai shekaru 69 da 'ya'ya 6 , a garin su na Umuofor a Karamar Hukumar Ogberuru na Jihar Imo state.
Hakan ya bar iyalansa da mutanen garin cikin kunci da zullumi rashin sanin halin da ya ke ciki. Sai gashi zullumin na su ya kau sakamakon Nasarar da 'yan sanda da jam'an sirri suka samu na kamo wanda aka fi zargi da sace Agha.
DUBA WANNAN: Kabilar Ibo: Kungiyar Ohanaeze ta yabi matasan arewa ta yadda suka mara ma zaman lafiya baya
An tasa keyar wanda ake zargi ya nuna inda suka binne Agha bayan sun kashe shi sakamakon bugun dawa da suka masa da sauran nau'ukan azaba.
Gawar ta Agha na sanye da ragowar tsummar rigar sa kuma fuskar ta na daure da kyallen da suka rufe masa ido da shi kafin su aika da shi lahira.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng