Dandalin Kannywood: Mijina ya bani zabin in koma fim amma na ki - Fati Ladan
Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood ta shaidawa duniya cewa babu wani aibu a cikin hada zaman aure da kuma yin sana'ar fim don kuwa abu ne mai yiwuwa.
Shahararriyar jarumar dai da tayi shuhura a wasu fina-finai da dama a da kafin tayi aure ta ce ita bayan ta yi aure mijin na ta ma ne ya bukaci ta ci gaba da sana'ar ta amma ita da kanta ta ki.
KU KARANTA: Abida Muhammad tayi magana game da yiwuwar dawowar ta fim
Legit.ng dai ta samu cewa haka zalika jarumar ta bayyana cewa yanzu ita kam tana zaman ta lafiya a gidan mijin ta inda ta ce ta samu cikakken kwanciyar hankali da nutsuwa.
Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa yanzu haka dai ta koma makaranta inda tuni ma har ta kai aji uku a tsangayar koyon kimiyyar siyasa kuma tana sana'ar ta ta kiwon kaji da kifaye.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng