Matana barauniya ce, kyamaran da na boye ya nuna ta na kwana da mazaje da yawa – Magidanci ya fada wa kotu
- Kotun ta raba aure mai tsawon shekaru takwas saboda zargin aikata laifin zina
- Alkali ya raba aure ne saboda zargi dake ya tsakanin ma'urata
- Mata ta zargi mijinta da kawo mata banza cikin gidan su
Wata Kotun al’ada na Mapo dake Ibadan ta raba aure da ya dauki tsawon shekaru takwas tsakanin wata mata mai suna Temitope Osunbote da mijinta Elijah, Saboda zargin aikata lafin zina.
Alkalin kotun, Ademola Odunade ya ce an raba auren ne saboda rashin yarda da zargi dake tsakanin ma’auratan.
Kotu ta ba matar Temitope damar rike yayan su biyu da suka Haifa, kuma kotu ta umarci Elijah ya rika biyar matar Naira N8,000 a kowani wata saboda kula da yayan.
“Wannan ya kunshi kula da karatun su da sauran bukatun su,” inji alkalin
KU KARANTA : Yan bindiga sun yi awon gaba da wani Majistare a jihar Kogi
Matar ta fada ma kotu cewa mijinta mazinaci wanda yake bin matan banza, kuma bai dauki auren su da daraja ba.
Yana kawo matan banza ciki gidan su duk lokacin da ya gadama, ko mutuncin ta baya gani.
“Da zarar nayi kuskure sai ya fara duka na. Kuma sai ya hana yayan mu abinci saboda fushi yaek yi da ni.
“Mutumin banza ne wanda ba san mutunci arue ba, kuma babu wata soyayya a tsakanin mu saboda haka ina kira da kotu ta raba mu.”
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng