Dandalin Kannywood: Ban sha'awar dawowa harkar fim ko kadan - Abida Muhammad

Dandalin Kannywood: Ban sha'awar dawowa harkar fim ko kadan - Abida Muhammad

Fitacciyar tsohuwar jarumar fina-finan Hausa ta masana'antar Kannywood Abida Muhammad ta bayyana cewa ko kadan bata sha'awar dawowa harkar shirya fina-finan Hausa kwata-kwata.

Fitacciyar jarumar ta bayyana hakan ne a zantawar ta da majiyar mu inda ta bayyana cewa tun da ta bar harkar ta tafi gidan mijin ta sai sana'ar ta bar bata sha'awa kwata-kwata.

Dandalin Kannywood: Ban sha'awar dawowa harkar fim ko kadan - Abida Muhammad
Dandalin Kannywood: Ban sha'awar dawowa harkar fim ko kadan - Abida Muhammad

KU KARANTA: Fati Muhammad ta shiga siyasa tsundum

Legit.ng dai ta samu cewa Abida Muhammad wadda ta haskaka sosai a lokutan baya musamman a cikin fina-finai da dama tayi aure da dadewa inda ta zauna a dakin mijin nata har Allah yayi masa rasuwa.

Masana harkokin fina-finai da dama dai na da ra'ayin cewa tsohuwar jarumar na daya daga cikin jaruman da Allah ya azurta da dimbin basira da ta bar gibin da kuma har yanzu ba'a cike ba a masana'antar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng