Kukan kurciya: Kalli yadda mutumin da Allah yayi ma ɗaukaka ke taimakon gajiyayye
Wani abin sha’awa daya faru a kasar Saudiyya tsakanin Sheikh Abdulrahman Sudai da wani gajiyayye zai burge ka tare da zama wa’azi ga duk mutumi mai hankali.
Wannan abu ya faru ne a Masallacin harami, inda bayan fitowar Sudais daga Masallaci yaci karo da wani mara lafiya dake zaune akan keken guragu yana neman wanda zai taimake shi ya tura shi, kamar yadda Dan Arewa ya ruwaito a shafin sa na Facebook.
KU KARANTA: Mu leƙa Kannywood: Ciwon dake damun jarumin Fim ɗin Hausa Warangis yayi kamari
Ganin haka keda wuya, sai Sheikh Abdulrahman Sudais ya dangana zuwa inda mutumin ke kikikaka, kuma ya bukaci ya tura shi, inda mutumin ya amince, shikenan suka kama hanya, askarawa kuma na basu kariya.
Ga wadanda basu sani ba, Sheikh Abdulrahman Sudais ne babbab limamin masallacin Makkah dake Harami, kusa da Ka’abah, wanda hakan ya bashi mukamin minista a gwamnatin Saudiyya.
Haka zalika Sudais na daya daga cikin mashahuran Musulman Duniya na wannan zamani, inda muryar karatunsa ke kayatar da miliyoyin musulmai da ma wadanda ba musulmai.
A shekarar 1961 aka haifi Sudais, ya haddace Qur’ani yana dan shekara 12, kuma ya fara limanci a Masallacin Makkah yana dan shekara 22 a shekarar 1984.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
We need to understand the Biafra objective, Legit.ng TV
Asali: Legit.ng