Jam’iyyar APC ta shiga cikin rudani a Jihar Katsina
- An samu baraka a Jam’iyyar APC mai mulki a Katsina
- Jam’iyyar ta rabe gida 2 da sunan Jam’iyyar APC Akida
- Ana kukan cewa Gwamnan Katsina ya hana APC gudu
Mun ji labari cewa an samu baraka a Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Katsina da sunan APC Akida kamar abin da ya faru a Jihar Katsina.
‘Yan APC Akida su na kukan cewa Gwamnan Jihar Aminu Bello Masari da hana Jam’iyyar ruwa gudu ta bakin Shugaban su Ahmed Himma Katsina. Barista Abbas Machika, Abdulaziz Labo Mahuta da Hajiya Murja Wambai su na cikin ‘Yan Kungiyar ta APC Akida.
KU KARANTA: Ba ni na raba buhunan shinkafa ba - Atiku
Sauran ‘Yan Kungiyar sun hada da manyan jiga-jigan APC a Jihar Sanata Sadiq Yar’Adua, Sanata Abdu Yandoma, Sanata MT Liman, Alhaji Sada Ilu, Dr Usman Bugaje, Tijjani Zangon Daura da Hannatu Musawa da irin su Gambo Musa Danmusa, Abubakar Samaila Isa Funtua, Kabir Murja.
Barista Abbas Machika yace dole su ceci Jam’iyyar a Jihar saboda ta kama hanyar rushewa. Sai dai na kusa da Gwamna Masari sun bayyana cewa ‘Yan APC Akidar surutun banza kurum su ke yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng