Fasaha! Wani matashi ya kera jirgi mai tuka kansa a garin Zariya
Wani haziki kuma fasiyin matashi dan asalin garin Zariya dake a jihar Kaduna na Arewa maso yammacin Najeriya mai suna Shatima Ali Kyari yayi abun azo-a-gani inda ya kera wani jirgi mai tashi sama tare kuma da tuka kansa.
Shi dai Shatima Ali Kyari kamar yadda muka samu daga majiyar mu dalibi ne a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya ya kuma kirkiro wannan jirgin nasa ne mai tuka kansa domin bajintar da Allah yayi masa.
KU KARANTA: Illar rashin bacci 7 ga dan adam
Legit.ng haka zalika ta samu cewa bayan kammala kera jirgin, matashin saurayin ya kuma yi gwajin sa inda ya saki jirgin yayi shawagi a sararin samaniya kamar dai yadda dama can ya tsara ba tare da wata tangarda ba.
Yankin Arewacin Najeriya dai cike yake da matasa masu matukar fasaha inda a baya ma muka kawo maku labarin wani matashin daga jihar Kebbi da ya kware sosai wajen kera motocin alfarma.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng