Yanzu Yanzu: Allah yayi ma tsohon gwamnan Kaduna Mouktar Muhammed rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah yayi ma tsohon gwamnan Kaduna Mouktar Muhammed rasuwa

Mouktar Muhammed, tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma babban jami’in soja mai ritaya ya rasu.

Mista Muhammaed, Air Vice Marshal mai ritaya, ya rasu a daren ranar Lahadi, a cewar wata sanarwa daga kaninsa, Faruk Dalhatu a shafin Facebook.

Jaridar Premium Times ta tattaro cewa Muhammed ya rasu a wani asibitin Landan.

Mista Dalhatu, wanda ya bayyana marigayin a matsayin jigon ahlin gidan Dalhatu ya bayyana musabbabin mutuwar sa a matsayin ciwon daji.

Yanzu Yanzu: Allah yayi ma tsohon gwamnan Kaduna Mouktar Muhammed rasuwa
Yanzu Yanzu: Allah yayi ma tsohon gwamnan Kaduna Mouktar Muhammed rasuwa

Jami’in sojan mai ritaya ya kasance gwamnan jihar Kaduna na farko bayan an kafa ta a shekarar 1977 a mulkin soja na Olusegun Obaanjo.

Da fari yayi aiki a matsayin ministan gidaje, cigaban karkara da muhalli daga 1976 zuwa 1977, bayan juyin mulki da ya kawo Murtala Mohammed kan mulki, wanda a ciki ya taka rawar gani.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi rashin gaskiya a jawabinsa na ranar yancin kai – Junaid Mohammed

Mista Muhammed ya kasance shugaban wani sauraren kararrakin zabe na mulkin soja dake hukunta yan siyasar jumhuriya ta biyu da aka zarga da cin hanci da rashawa a karkashin gwamnatin Muhammadu Buhari na soja, daga 1983 zuwa 1985. An tura da dama daga cikin yan siyasa gidan yari na yan wasu shekaru.

A shekara ta 1985, mista Muhammed bai dade a mulki ba bayan zuwan gwamnatin Babangida, sakamakon rashin amincewa da juyin mulki da akayi ma Mista Buhari.

A shekarar da ta gabata, aka nada shi shugaban kungiyar masu kula da jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.

Har mutuwarsa, Mista Muhammed wanda ke rike da sarautar Wazirin Dutse ya kasance mataimakin shugaban kungiyar amintattun arewa, ACF.

Ya kuma kasance shugaban gidan radiyon Freedom dake Kano.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng