Damisa, ƙi sabo: Wani dabban daji yayi kaca kaca da wani mutumi a garin Ibadan

Damisa, ƙi sabo: Wani dabban daji yayi kaca kaca da wani mutumi a garin Ibadan

Ajali kenan, idan yayi kira ko ba ciwo sai an je, kuma yadda duk yadda Allah ya nufa dan Adam zai mutu, toh fa ba makawa, sai ya mutu, don kuwa ko sa’a guda ba za’a kara masa ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito wani mummunan lamari daya faru a garin Ibadan dake jihar Oyo, inda Maigadin gidan ajiyan dabbobi dake cikin garin Ibadan ya gamu da ajalinsa a hannun wani Zaki dake ajiye a gidan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya bani muhimmiyar shawara dangane da zaɓen 2019 – Inji Nasir El-Rufai

A ranar 30 ga watan Satumbar data gabata ne wannan lamari ya faru a gidan Zoo dake Agodi, inda Zakin ya kai farmaki ga daya daga cikin masu kula da shi, wani mutumi mai suna Hamzat Oyekunle.

Damisa, ƙi sabo: Wani dabban daji yayi kaca kaca da wani mutumi a garin Ibadan
Zakuna

Mutumin da aka fi sani da suna Baba Olorunwa ya gamu da ajalinsa ne yayind a Zakin ya afka masa, inda ya ji masa rauni sosai da sosai, inda ko da aka garzaya da shi Asibiti, a can yace ga garinku nan.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito faruwan wannan mummunan lamari ya sanya gwamnatin jihar sanar da rufe gidan ajiyan dabbobin, bayan data samu rahoto daga kamfanin dake kula da gidan, AM&C.

Zuwa yanzu dai an dauke dabbar, sa’annan gwamnatin jihar ta umarci a gudanar da binciken yadda lamarin ya wakana, don kare sake faruwar hakan, sa’annan ta aika da tawagar ta zuwa ga iyalin mamacin don jajanta musu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng