Abubuwa 10 masu muhimmanci daga jawabin Buhari a sakon bikin murnar ‘yancin kai

Abubuwa 10 masu muhimmanci daga jawabin Buhari a sakon bikin murnar ‘yancin kai

- Shugaba Buhari ya ce ranar 1 ga watan Oktober rana ce na musamman ga dukan 'yan Najeriya

- Shugaban kasar ya tabbatar cewa gwamnatinsa na kokari ta yadda za a sake sauran 'yan matan Chibok da suke hannun ‘yan Boko Haram

- Buhari ya ce za a hanzarta ci gaba da kuma magance matsalolin da kasar ke ciki

Wasu daga cikin abubuwa masu muhimmanci a jawabin shugaban kasa Muhammadu Buhari a sakon murnar ‘yancin kai ga ‘yan Najeriya a yau Lahadi, 1 ga watan Oktober.

1. Ranar 1 ga watan Oktoba ta kasance kwanan wata na musamman ga dukan 'yan Najeriya

2. A cikin shekaru da dama kasar ta shiga cikin wani halin kakani kayi da kuma matsaloli, amma kowane ranar 1 ga watan Oktoba wata rana ne na biki a kasar

3. Ranar 1 ga watan Oktoba na kowane shekara ranar ce ta tunawa a Najeriya

Abubuwa 10 daga jawabin Buhari a sakon bikin murnar ‘yancin kai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

4. Dole ne a daidaita arzikin kasar don kada mu dogara ga man fetur kadai

5. Dole ne mu yaki cin hanci da rashawa wanda yake shi ne na farkon makiya ga Najeriya

6. Kira na kwanan nan game da sake tsarin mulkin Najeriya, wanda ya dace, amma kungiyoyi a wasu yankunan kasar na amfani da wannan dama wajen neman raba kasar. Ba za mu amince da haka ba kuma ba za mu bari irin wannan ya ci gaba ba

KU KARANTA: Labari cikin Hotuna: Yau ga Baba Buhari a filin daaga; Maiduguri ta karbi shugaban kasa

7. A matsayin matashi na soja, da ni aka fara yakin basasa daga farko har zuwa ƙarshen ta wanda ta yi sanadiyar mutuwa kimani mutane miliyan 2.

8. Wadanda ke neman haddasa sabuwar yaki yanzu, ba a haife su ba ne a 1967, kuma ba su da masaniya game da mummunar tashin hankalin da kasar ta fuskanta.

9. Gwamnati na iya kokarin ta kowane lokaci domin tabbatar da saki sauran 'yan matan Chibok da suke hannun ‘yan Boko Haram

10. Tare da yawan ruwan sama a bara da wannan shekara, aikin noma a kasar ta samu taimakon Allah

Legit.ng ta tattaro cewa, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yayin da aka shiga rabi na wa’adin gwamnatinsa, za a hanzarta ci gaba da kuma magance matsalolin da kasar ke ciki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng