Kungiyoyi 10 ma su karfin gaske a Najeriya

Kungiyoyi 10 ma su karfin gaske a Najeriya

Legit.ng ta kawo muku jerin kungiyoyi masu karfin gaske, wanda ke girgiza ko wace irin gwamnati a yayin da kungiyoyin kasuwanci suka zamto jigo a cikin masana'antu da dama na fadin duniyar nan.

A nan Najeriya, ma'aikata na da kungiyoyi daban-daban da suke aron bakunan mambobin domin su ci musu albasa daidai da tsaruka na wannan masana'antu. Wanda manufar hakan shin domin kowace kungiya ta kare hakkokin mambobin ta.

Akwai kungiyoyi da dama a fadin Najeriya wanda suke da hadin gwiwa a karkashin kungiyoyin na biyu na kungiyar kwadago ta kasa (Nigeria Labour Congress, NLC) da kuma kungiyar masana'antu (Trade Union Congress, TUC).

A yayin haka cikin shekaru na kwana-kwanan nan, wasu kungiyoyin sakamakon irin dabaru da tsare-tsarensu da kuma rawar da suke takawa, sun yi wasu kungiyoyi zarra wajen sauraronsu a cikin al'umma.

Kungiyoyi 10 ma su karfin gaske a Najeriya
Kungiyoyi 10 ma su karfin gaske a Najeriya

Makamanciyar barzana da kuma yajin aiki da za su iya fadawa a cikin kowane irin hali da bai daidai da bukatunsu ba, ya sanya gwamnati da al'umma suke sauraro da kuma ba su hankulansu wajen jin bukatun su.

Wasu kungiyoyin sabili da irin karfin da suke da shi, su na iya yiwa gwamnati rikon kazar kuku da har sai ta yi kokarin fansar kanta wajen biyan bukatun wannan kungiya domin idan ba haka za su janyo barazan ga tattalin arzikin kasa ko kuma zagon kasa ga gudanarwa da al'amurran aikace-aikace na kasa.

KARANTA KUMA: An kaiwa wani Kwanturola na hukumar Fasakauri hari a jihar Ogun

Legit.ng ta kawo tattaro muku jerin kungiyiyo 10 wanda nasabar su ta kai wani munzali da ka iya girgiza gwamnatin Najeriya sakamakon irin tasiri da kuma karfi wajen mamaye dukkan harkokin gudanarwa a fadin kasar nan.

1. NLC: Nigeria Labour Congress

NLC is an umbrella organisation for trade unions in Nigeria. It was founded in 1978 following a merger of four different organisations: Nigeria Trade Union Congress, NTUC; Labour Unity Front, LUF; United Labour Congress, ULC; and Nigeria Workers Council, NWC.

1. Kungiyar kwadago ta kasa (Nigeria Labour Congress, NLC)

2. Kungiyar ma'aikatan man fetur da gas ta kasa (National Union of Petroleum and Natural Gas Workers, NUPENG)

3. Kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da gasa ta Najeriya (Petroleum and Natural Gas Senior Staff Assocition of Nigeria, PENGASSAN)

4. Kungiyar Lafiya ta Najeriya (Nigerian Medical Association, NMA)

5. Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (Academic Staff Union of Universities, ASUU)

6. Kungiyar malaman makaranta ta Najeriya (Nigeria Union of Teachers)

7. Kungiyar ma'aikata marasa koyarwa na jami'o'i (Non-Academic Staff Union of Universities, NASU)

8. Kungiyar malaman makarantun ci gaba da karatu (Academic Staff Union of Polytechnics, ASUP)

9. Kungiyar likitoci ta kasa (National Association of Medical Doctors, NARD)

10. Kungiyar masana'antun kasuwanci ta Kasa (Trade Union Congress, TUC)

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng