Nayi mamakin dumbin masoyan da na - mahaifiyar marigayi Lil Ameer
Hajiya Maimuna Hassan dake zaman mahaifiyar marigayin dan autan mawakan Hausa na Hip HoP a arewacin Najeriyar nan watau Lim Ameer ta bayyana matukar mamakin ta ga irin dumbin magoya bayan da dan nata ke da su a fadin Najeriya da duniya baki daya.
Mahaifiyar ta marigayin ta bayyana cewa irin yawa sakonnin ta'aziyyar da muka samu da kuma alhini daga ko wane sako na duniya yayi matukar kadanin don kuwa ban ma san yayi irin wannan shaharar ba.
KU KARANTA: Takaicin maza ke sa mata shaye-share
Legit.ng ta samu kuma cewa mahaifiyar marigayin daga nan ne kuma sai ta mika sakon godiyar ta ga dukkan wadan da suka nuna alhinin su kuma suka tausaya musu dangane da rasuwar dan nata ta kuma yi addu'ar Allah ya jikan dan nata da dukkan yan uwa musulmai baki daya.
Haka nan kuma sai mahaifiyar ta jawo hankalin iyaye da su ba yayan su damar zabar hanyar rayuwar su ba tare da tsangwama ko kyara ba don kuwa basu san irin baiwar da Allah ya basu ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng