An fitar da sunayen sabbin Malamai 178 da gwamnatin jihar Katsina ta ɗauka
- Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sunayen sabbin Malamai data dauka aiki
- Yawan Malaman da aka dauka ya kai 178
A ranar Alhamis, 28 ga watan Satumba bayan an yi tankada da rairaye ne aka fitar da jerin sunayen sabbin Malamai da gwamnatin jihar Katsina ta dauke su aiki don koyarwa a makarantun jihar.
Wani ma’bocin kafar sadarwar zamani na Facebook, Muhd Liman ne ya bayyana haka a shafinsa, inda ya daura hotunan sunayen sabbin Malaman da aka dauka.
KU KARANTA: Yan bindiga sun sace mataimakin kwamishinan Yansanda tare da iyalansa su 3
Malaman da yawansu ya kai 178 an dauke su ne a karkashin tsarin maye gurbin Malaman jihar da suka bar aiki, ko suka rasu, ko kuma suka samu sauyin aiki.
Kimanin watanni biyu da suka gabata ne jama’a da dama masu sha’awar samun aikin koyarwar suka zana jarabawar neman, aikin, inda aka yi tankada da rairaye, don fitar da mutanen da suka fi cancanta.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng