Rikita-Rikita: Hatsabibi Nnamdi Kanu fa ya bace bat inji yan sandan jihar Abia

Rikita-Rikita: Hatsabibi Nnamdi Kanu fa ya bace bat inji yan sandan jihar Abia

Rundunar 'yan sandan jihar Abia dake a kudu maso gabashin Najeriya , ta bayyana cewa bata da wata masaniya akan inda madugun kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu yake a halin yanzu da ake ci gaba da tofa albarkacin baki a kan batun a kudancin Najeriya.

A wata hira da suka yi da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka, Alphonsus Okoroigwe, Kwamishinan rundunar 'yan sandan jihar Abia, Mr Anthony Okwueze, ya bayyana cewa basu da masaniya akan inda Nnamdi kanu yake.

Rikita-Rikita: Hatsabibi Nnamdi Kanu fa ya bace bat inji yan sandan jihar Abia
Rikita-Rikita: Hatsabibi Nnamdi Kanu fa ya bace bat inji yan sandan jihar Abia

KU KARANTA: An bankado wani wurin atisayen sojoji na bogi

Legit.ng ta samu dai cewa jami'in ya bayyana cewa da suna da masaniya da sun fahimtar da shi akan tunani mai armashi, dan haka ya kara da cewa idan manema labarai na da masaniya, akwai bukatar su shaidawa jami'an domin tafiya tare wajan shawo kan lamarin.

Lamarin batan dabon da madugun kungiyar ya yi ya haifar da musayar ra'ayoyi a tsakanin jama'ar jihar, Mr Moses Okoye, wani dan kasuwa ne kuma ya bayyana cewa tana iya yiwuya Nnamdi Kanu na raye ko kuma baya raye ganin yadda sojoji suka kai hari a fadar mahaifinsa, dan haka idan yana raye a taimaka a sake shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng