Labari Cikin Hotuna: Jami'an 'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane da 'yan fashi da makami
Sakamakon simame da fafutikar wanzar da zaman lafiya a kasar nan, 'yan sandan Najeriya sun samu nasarar cafke wasu gaggan 'yan fashi da makami da kuma masu garkuwa da mutane da neman kudin fansar su.
'Yan sandan sun samu nasarar damkar mutane 31 da ake zarginsu da aikata wannan laifuka, wadanda suka addabi manyan hanyoyin Abuja zuwa Minna da kuma hanyar Abuja zuwa Kaduna daura da kauyen Dikko dake garin Suleja a jihar Neja.
Legit.ng ta fahimci cewa, sakamakon wani simame da masu garkuwa da mutane suka yi wa jami'an 'yan sanda a ranar Talata 26 ga watan Satumba, ya yi sanadiyar ran wani Sajen Shettima Abdullahi, wanda kuma musayar wuta tsakanin jami'an 'yan sanda da 'yan ta'addan ya salwantar da rayuka 5 na masu garkuwa da mutane.
Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya CSP Jimoh Moshood, ya rubuto sunayen 'yan ta'addan har guda 31 da hukumar ta yi nasarar cafkewa wanda cikinsu guda biyar sun sheka lahira. Ya kuma bayyana cewa yawancin 'yan ta'addan su na amfani da kakin soja wajan gudanar da wannan ta'asa ta su.
Ya kawo sunayensu kamar haka:
1. HUSSAINI MOHAMMED (Inkiyarsa Janar Maigemu Sambisa) Shugaban gangamin 'yan fashin
2. ADAMU HUSSAINI
3. BALA MOHAMMED
4. SHAGARI MUSA
5. HASSAN HASHIMU
6. IBRAHIM BADAMASI
7. BABANGIDA HAMZA
8. YA'U AUTA
9. ALH. UMARU ABUBAKAR
10. KARO LADAN
11. BUHARI ABUBAKR
12. ALANSHIRA ABUBAKAR
13. AZIRU TASIU
14. IBRAHIM MUSA
15. ISHAMU SAIDU
16. SANI ALIYU
17. SHUAIBU ABUBAKAR
18. BASHIR ABUBAKAR
19. NASIRU SANI
20. ZAYANU SANI
21. ISA SALISU
22. HAFIZ JIBRIN
23. KABIRU SANI
24.ABDULLAHI ADAMU mai inkiyar DARE
25. BARA'U MASAUDU
26. IBRAHIM HASSAN
27. ALIYU CHEDE
28. BELLO ABDULLAHI
29. ISA ABDULAHI
30. NASIRU ADAMU
31. IDRIS DAUDA
Nasarar cafke wannan 'yan ta'adda ya bayu ne sakamakon umarnin Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim K. Idris akan jami'an su gurfana domin kawo karshen ta'addaci da faskara a wannan manyan hanyoyi, wanda hakan ya sanya aka fatattako su daga mabuyarsu tare da mallakin kayayyaki daban-daban wadanda suka hadar da bindigu, na'urori mai kwakwalwa, na daukan hoto, na daukan sauti da kuma talabijin.
KARANTA KUMA: Fayose zai ƙaddamar da takarar sa ta kujerar shugaban ƙasa a ranar Alhamis
Akwai ire-iren wayoyin sadarwa, katin karbar kudi na bankuna da kuma makamai da dama da hukumar 'yan sandan ta samu a wajen wannan 'yan ta'adda, baya ga motoci na jama'ar da suka karba.
Shugaban na 'yan sanda ya bayyana cewa wannan 'yan ta'adda sun amsa laifukansu, yayin da wasu su daga cikinsu suka ce har fyade sun yiwa wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su ko kuma fashi da makami. Ya kara da cewa, hukumar ta 'yan sanda za ta cigaba da gudanar da binciken akan wannan 'yan ta'adda kafin ta mika su ga kotu domin gurfanarwa.
Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng