Dan hakin daka raina: Kalli yadda kuɗin Cizo ya tasa ɗaliba jami’a a gaba
Kamfanin jaridar Legit.ng ta ci karo da wasu daliban jami’a wadanda kudin Cizo ya addabe su, wanda hakan ya sanya su shiga mayuwacin hali, inda ko kwanan daki wasu basa yi.
Daliban da suka fito daga jami’ar Obafemi Awolowo sun koka kan cewa kudin cizo sun mamaye dakunan kwanan dalibai dake cikin makarantar, inda suka ce sun yi katutu cikin katifunsu.
KU KARANTA: Fayose zai ƙaddamar da takarar sa ta kujerar shugaban ƙasa a ranar Alhamis
Wata dalibar jami’ar, Michael Kalis Oluwatobi ta bayyana yadda hukumar makarantar ke kokarin ceto su daga halin ni yasun.
Sai dai Oluwatobi tace an yanke shwara a tsakanin dalibai da kowa ya fitar da katifansa waje don su sha rana, ko hakan zai taimaka wajen rage yawan kudin cizon.
Sai dai daga karshe hukumar jami’ar ta bada umarnin yin feshi a dakunan dlaibai da sauran wuraren da daliban ke kwana, don magance kudin cizon.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng