Dubi jerin kasashe 9 masu makamin kisan kare dangi na nukiliya
Adadin makamin nukiliya na duniya na raguwa, misali, adadin makamin nukiliya na duniya 70,300 ne a shekarar 1986, amma ya ragu zuwa 16,300 a shekarar 2016.
Mun kawo maku jerin kasashe 9 masu makamin nukiliya ne saboda yawaitar kara samun sa-toka-sa-katsi a 'yan kwanakinnan tsakanin kasar Amurka data Koriya ta arewa domin kuyi alkalanci a kan wannan dambaruwa tsakanin kasashen biyu da kuma siyasar dake cikin mallakar makamin na nukiliya.
Ga jerin kasashen 9 masu makamin kisan kare dangi na nukiliya
1. Rasha
Adadin makamin nukiliya masu amfani: 1,9101
Adadin makamin a ma'adana: 2,390
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 2,700
Jimillar makamin nukiliya: 7,000
2. Amurka
Adadin makamin nukiliya masu amfani: 1,800
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 2,200
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 2,800
Jimillar makamin nukiliya: 6,800
3. Faransa
Adadin makamin nukiliya masu amfani: 290
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 10
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 0
Jimillar makamin nukiliya: 300
4. CHINA
Adadin makamin nukiliya masu amfani: Babu tabbas
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 270
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 0
Jimillar makamin nukiliya: 270
5. Ingila
Adadin makamin nukiliya masu amfani: 120
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 95
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 0
Jimillar makamin nukiliya: 215
6. Pakistan
Adadin makamin nukiliya masu amfani: 0
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 140
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 0
Jimillar makamin nukiliya: 140
DUBA WANNAN Zaben Kasar Jamus da aka kammala jiya: 'Yan Kasar Jamus Basa Zaben Shugaban Kasa Kai tsaye, duba nasu tsarin zaben
7. Indiya
Adadin makamin nukiliya masu amfani: 0
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 80
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 0
Jimillar makamin nukiliya: 80
8. Isra'ila
Adadin makamin nukiliya masu amfani: 0
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 130
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 0
Jimillar makamin nukiliya: 130
9. Koriya ta arewa
Adadin makamin nukiliya masu amfani: Babu tabbas
Adadin makamin nukiliya a ma'adana: 60
Adadin gajiyayyun makamin nukiliya: 0
Jimillar makamin nukiliya: 60
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng