Assha! Madarar sukudaye ta yi sanadiyyar ajalin wani matashi a Zariya
A makon da ya gabata ne wani matashi mai suna Abubakar Dan Zamfara, ya mutu da kwalbar madarar Sukudaye a hannunsa a wata unguwa da ake kira unguwar Liman da ke garin Samaru a Karamar Hukumar Sabon Garin Zariya ta Jihar Kaduna.
Shi dai wannan matashin mai suna Abubakar Dan Zamfara dan kimanin shekaru 25 ne a duniya. Ya zo garin samara ne don neman aikin yi, daga jihar Zamfara.
KU KARANTA: Kasar Iran tayi gwajin makamin Nukiliya
Legit.ng ta samu dai cewa hakan ya sa ya nemi wajen zama a wannan unguwa da ake kira Unguwar Liman a wani gida da yake da dakuna ta waje. Wanda asalin dakin na wani abokin sa ne da shi ma ya zo kadar rama, amma da tafiyar tasa ta yi riba sai yayi aure ya bar wa Abubakar dakin ya ci gaba da biyan kudin haya.
Abubakar kafin mutuwar tasa yana aiki ne a wani wajen wanke motoci da ke Zangon Shanu, hayin Samarun zariya. Ana zargin cewa a duk lokacin da ya dawo daga wajen aiki ne ya ke sayo madarar ta sukudaye sai ya je daki ya kwankwade ta kafin ya kwanta barci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng