Barazanar Yaki: Cacar baki tsakanin kasar Amurka da Korea ta Arewa ta ci gaba
- Shugabannin kasashen Amurka da na Korea ta Arewa wato Donald Trump da Kim Jong Un, sun ci gaba da jifan junan su da kalaman batanci.
- Trump ya ce, ''Kim Jong Un mutum ne mai roka wanda ke kan tafarkin halaka kan sa''
- Kim kuma ya ce, ''Trump mai tabin hankali ne da giyar mulki ke dibar sa''
Shugaban kasar Amurka Donald trump a yayin jawabin sa na taron Majalisar Dinkin Duniya da ya gabata ya kwatanta Shugaban Kasar Korea ta Arewa a matsayin ''mutum mai roka'' wanda ke kan tafarkin halaka kan sa.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne Trum ya rubuta a shafin sa na twitter cewan, '' Kim Jong Un na Korea ta Arewa, mutum ne mai tabin hankali. Azabtar da mutanensa da yunwa, da kashe su da yake yi basu dame shi ba. Zai ga jarrabawar da bai taba ganin irin sa ba a baya.”
DUBA WANNAN: Hotuna: Gwamna Ganduje zai gina katafaren kamfanin sarafa tufafi na Dala Miliyan 600 tare da hadin gwiwar kasar China
Trump har ya kai ga kiran gwamnatin Kim a matsayin gwamnatin azzalumai. Ya kuma jaddada cewa Amurka za ta kare kanta da kawayenta idan akwai bukatar hakan, za ta shafe Korea ta arewa daga doron kasa baki daya.
Shugaban Korea ta Arewa ya mayar da martini ta bakin Ministan harkokin wajen kasar mai suna Ri Yong wanda ya gabatar da jawabi a taron Majalisar in da ya kwatanta Trump a mtsayin mutum mai tabin hankali da giyar mulki ke diban sa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng