Bayyanar nau'in damisar 'Leopard' a Yankari zai dawo da martabar gidan gandun dajin

Bayyanar nau'in damisar 'Leopard' a Yankari zai dawo da martabar gidan gandun dajin

- An ga wannan damisa ne a hoto da na'urar daukan hoto da ke cikin dajin ya dauka

- Shekaru da dama rabon da a ga irin wannan damisa har ta kai ga an yi tsammanin babu sauran irin su a dajin na Yankari

- Haka ma wata kyanwar daji mai suna Caracal Cat ta bayyana. Bayyanan dabbobin da aka dade ba'a gan su ba zai dawo da martaban dajin na Yankari

A kwanakin baya ne damisa nau'in leopard ya bayyana a dajin Yankari na Jihar Bauchi. John Umar mai kula da dajin da kuma hotunan da na'urar daukan hoto ke dauka akai akai a wurare daban daban na dajin don kare dajin daga farmakin barayin mafarauta ne ya yi katarin ganin damisan a cikin hoto.

Irin wannan damisa dai shekaru da dama aka yanke tsammanin ganin su a dajin. An dauki wanann hoto ne a kusa da tsaunin Tonglong da ke dajin wanda wuri ne da dabbobin daji irin su kura da dila da yanyawa ke zama. Bayynan damisan babban al'amari ne saboda mutane sun fi sabawa da nau'in damisan Tiger da Cheetah.

Dajin Yankari ya fara dawowa da tagomashin sa, bayan dabobi da suka bace suka fara dawowa
Dajin Yankari ya fara dawowa da tagomashin sa, bayan dabobi da suka bace suka fara dawowa

Babban mai kula da dajin, Injiniya Habu Mamman ya ce wata nau'in kyanwar daji wanda a turance ake kira Caracal Cat ita ma ta bayyana amma bayyanar nata bai kai shaharan bayyanan damisan ba. Bayyanan wadannan dabbobi yana alamta yiwuwan akwai wasu dabbobin da dama da suke dajin wanda aka yi tunanin sun kare.

DUBA WANNAN: Ambaliyar ruwa ya mamaye gonakin shinkafa 450 a Kwara

Da jin wannan labari mutane masu sha'awan dabbobin daji suka tofa albarkacin bakunan su kuma suke ta kwadayin zuwa ganin wannan damisa wanda hakan zai dawo da martaban dajin na yankari.

Hukumar kula da dajin ta ce ya zama dole ta karfafa tsaro ta kuma wayar da kan ma'aikatan ta da kuma jama'a masu ziyara kasancewar Damisar Leopard dabba ce mai hatsarin gaske. Har wayau Hukumar zata karfafa tsaro don kare damisar daga farmakin barayin mafarauta.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164