Shugaban kasar Philippines ya bada iznin a kashe yaron sa

Shugaban kasar Philippines ya bada iznin a kashe yaron sa

- Shugaban Philippines yace idan har an samu yaron sa da laifi a hukunta sa

- Rodrigo Duterte na kasar ba ya wasa da harkar miyagun kwayoyi ko kadan

- An dai kashe sama da mutane 9000 a Garin wanda ya jawo surutu a ko ina

Idan ku na tare da mu za ku san cewa Shugaban kasar Philippines dai ya sa kafar wando daya da masu harkar miyagun kwayoyi a Kasar sa.

Shugaban kasar Philippines ya bada iznin a kashe yaron sa
Shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte

Sai ga shi dai kwanan nan ana zargin babban Dan Shugaban kasar Paolo Duterte da laifin harkar safarar miyagun kwayoyi wanda Shugaban kasar da kan sa ya ba 'Yan Sanda umarnin cewa idan ta tabbata an samu 'Dan da ya haifa mai shekaru 42 da rashin gaskiya su aika sa lahira.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kara kaimi wajen yaki da sata

Shugaban kasa Rodrigo Duterte ba ya wata-wata idan aka zo maganar miyagun kwayoyi wanda kawo yanzu Gwamnatin sa ta kashe zama da mutane 9000 da aka kama da laifin safarar kwayoyi wanda ta sa wasu kasashen Duniya tayi ca a kan sa.

Kwanaki aka samu Fabio Lobo dan gidan tsohon shugaban kasar Honduras Porfirio Lobo da laifin safarar miyagun kwayoyi. Tuni dai an yanke masa daurin shekaru 24 a kurkuku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko ayi cewa maza masu auren Hajiyoyi sun zama 'Yan kasuwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng