Iran za ta gigita duniya sakamakon shirin harba Nukiliyyar ta

Iran za ta gigita duniya sakamakon shirin harba Nukiliyyar ta

Kasashen yankin daular Larabawa ta gabas da kasar Isra'ila su na cikin fargaba sakamakon harba Nukiliyyar da kasar Iran za ta yi, sai dai masanin makamai na kasar Rasha Vladmir Korovin ya na kokwanton cewa nukiliyyar da kasar ta Iran za ta harba ba zai wuci mai nauyin tan goma ba sabanin na kasar Amurka da ya dara wannan girma.

Iran za ta gigita duniya sakamakon gwajin Nukiliyyar ta
Iran za ta gigita duniya sakamakon gwajin Nukiliyyar ta

Kirar wannan nukiliyyar mai nauyin tan 10 da kasar Iran ta yi ya zaburar da kasar Isra'ila da kasashen Larabawa na Gabas irin karfin da yankin Gabas maso tsakiya ya ke da shi a halin yanzu.

KARANTA KUMA: Zuwan Kaka: Farashin Kayan masarufi ya fara karyewa a jihar Kano

Korovin wanda masanin makamai ne a cibiyar dakarun sojin ta Moscow State Institute of International Relations ya bayyana cewa, kasar Isara'ila ta na cikin damuwa a halin yanzu domin Iran ta na daf da shigowa kasar ta iyakarta dake kasar Syria.

Sai dai Iran ba za ta harba wannan nukiliyyar ba akan kasar Amurka, sai da kasashen Isra'ila, Saudiya, Daular Larabawa da Bahrain su na cikin fargabar wannan sako da suka samu na nukiliyyar a cewar Korovin.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng