Zuwan Kaka: Farashin Kayan masarufi ya fara karyewa a jihar Kano

Zuwan Kaka: Farashin Kayan masarufi ya fara karyewa a jihar Kano

Sakamakon zuwan Kaka da manoma ke girbo amfanin gonakinsu a jihar Kano, farashin kayan masarufi ya fara faduwa wanwar duba da tashin doron zabi da farashin ya yi a makonnin da suka gabata.

Shafin Kano Chronicles ya ruwaito cewa an fara girbin amfanin gona irinsu, wake, gyada, masara, shinkafa da gero wanda hakan ya sanya farashin kayan masarufin suke faduwa wanwar.

Legit.ng ta fahimci cewa a sakamakon ziyarce-ziyarce kasuwanni da manema labarai suke yi, an samu rahoton farashin buhu masara a kasuwar Dawanau wanda a da can yake Naira 15, 000 yanzu ya koma Naira 8, 500, buhun gero ya fado daga naira 15, 500 zuwa naira 9, 000 da kuma buhun shinkafar hausa daga Naira 32, 000 zuwa Naira 29, 000.

Kaka: Farashin Kayan masarufi ya fara karyewa a jihar Kano
Kaka: Farashin Kayan masarufi ya fara karyewa a jihar Kano

Sai kuma kasuwar Tarauni inda binciken manema labarai ya nuna cewa, buhun dankalin turawa ya fado daga naira 22, 000 zuwa 18, 000 sai dai har yanzu farashin kwando yananan a naira 1, 200 da kuma buhun dankalin hausa daga naira 11, 000 zuwa naira 7, 000.

KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Dalibai sun gudanar da zanga-zanga a jihar Borno

Binciken jaridar Kano Chronicles ya nuna cewa har yanzu dai buhun sukari yana nan a farashinsa na naira 18, 500 da kuma awo dayansa yake a farashinsa na 1, 200.

Wani mai sayar da tumatiri Malam Yusha'u Umar ya bayyanawa manema labarai cewa, "lallai farashin kaya masarufi ya fado ba kamar makonni biyu ko uku da suka gabata ba, domin ko kwanon tumatir wanda a da ake sayar da shi akan kudi Naira 1000 zuwa 2000 yanzu ya koma Naira 400 wanda idan ciniki ya yi ciniki ana sayar da shi a kasa da haka".

Sai dai duk da faduwar farashin kayan masarufin, da yawan 'yan kasuwan su na kukan rashin samun ciniki a kasuwannin na su.

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: